Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuAn hana babbar kawar amarya shiga biki saboda shigarta yafi na Amaryar...

An hana babbar kawar amarya shiga biki saboda shigarta yafi na Amaryar kyau

Daga Muryoyi

Wata Amarya a Jamus ta kwace katin gayyatar daya daga cikin kawayenta saboda ta caba kwalliya da shiga ta kece raini har ta fi na amaryar kyau.

Kodayake taki fadin sunan amaryar amma kawar mai suna Alena Yildiz ta ce Amaryar ta yi mata rashin mutunci ta hana ta shiga liyafar bikinta saboda tayi shiga “mai daukar hankali sosai”

Muryoyi ta ruwaito Alena Yildiz ce ta fallasa labarin cin mutuncin da kawar tata tayi mata a shafinta na Instagram inda tace daga cikin su 6 kawaye ita kadai aka maida saniyar ware aka hana ta shiga wajen liyafar bikin.

- Advertisement -

A cewarta ita da amaryar kawayene na kud-da kud kuma ita amaryar ce ma da kanta ta zabar mata kayan da za ta saka a bikin nata amma kuma tayi mata wulakanci daga baya.

Yildiz ta ce ‘kawar tawa taji tsoron nayi kyau sosai hankali zai karkata akaina.’ A cewarta duk sauran kawayen sun caba ado sosai da kaya na alfarma da kece raini amma duk bata da matsala dasu sai nawa!

Yildiz ta cigaba da cewa duk da haka nayi hotuna da shigar tawa. Tace nayi mamaki idan tasan kayan zasuyi mana kyau sosai mai yasa ta zabo mana su a matsayin anko ai da sai ta zabo munanan kaya muyi anko dashi”


Sai dai hakan bai yi wa kawar dadi ba inda a yanzu suka raba jiha domin tana ganin babu amfanin kawancen nasu “kenan babu amfanin kawancen”

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: