Daga Muryoyi
An kama wani dan bindiga dauke da jerin sunayen mutanen da zai kashe a hanyarsa ta shiga ginin White House fadar shugaban kasar Amurka
Muryoyi ta tattaro rahotanni daga kafafen yada labarai a Amurka cewa a cikin jerin sunayen mutanen da dan bindigar zai kashe har da Shugaban kasa mai ci Joe Biden, da tsohon shugaban kasa Clinton da Obama da shuganan Facebook (Meta) Mark Zuckerberg da Anthony Fauci da sauran su.
An gurfanar da mutumin mai suna Kuachua Brillion Xiong, daga jihar Merced, California bayan an sami bindiga kirar AR-15-type da harsasai masu yawa da rigar sulke, da akwatin magani da sauran kayan kai hari
- Advertisement -
Sashin tsaron farin kaya na Amurka Justin Larson ya fitar da sanarwar cewa za a gurfanar da Xiong a gaban kuliya a ranar Alhamis
Jaridar Times ta kasar Amurka ta ruwaito cewa mutumin yace yayi bankwana da iyalansa kuma ba zai koma ba har sai ya halaka bakaken shedanu yan siyasa da suka jefa kasar Amurka cikin mawuyacin hali.
Muryoyi ta ruwaito an kama mutumin ne a wani shingen bincike ya nufi White House bayan bincike aka samu makamai a motarsa da kuma jerin sunayen wadanda zai halaka “kuma ya lashi takobin ko mai zai faru sai ya aiwatar da abunda yayi nufi muddin aka sake shi”
Xiong dan Shekara, 25 an gurfanar dashi a gaban Kotun Pottawattamie County dake Iowa a ranar 21 ga watan Disamna 2021.
Larson ya ce za a cigaba da tsaron mutumin sannan zai gurfana a gaban kotu yau Alhamis