An kama gidan masu garkuwa da mutane kusa da shingen binciken yan sanda a hanyar Abuja 

Daga Muryoyi

An bankado wani gidan da masu garkuwa da mutane ke kama mutane suna boyewa a wani kauye dake kan babban titin Auchi zuwa Abuja,

Muryoyi ta ruwaito abun ya tada hankalin mazauna kauyen domin akwai shingen bincike na yan sanda da suke binciken ababen hawa da mutane a bayan gidan da aka kaman.

A bidiyon da ya karade kafafen yada labarai an kama albarusai da jarkoki da barkonon saka hawaye da sauran makamai jibge a cikin gidan mai dakuna kusan 3, Muryoyi ta ruwaito gidan ginin kasa ne amma kuma a gefen titi akayi shi dab da cikin daji,

- Advertisement -

Kafin a bankado wajen a ranar Alhamis 2 ga watan Disamba dai mazauna kauyen sun ce wani mahaukaci ne ke zama a cikinsa ana yawan ganin sa a harabar,

Asirin gidan ya tonu ne bayan da aka yi garkuwa da wata Bas jibge da matafiya.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: