Daga Muryoyi
Shugaban yan sandan Najeriya IGP Alkali Usman Baba ya ce an samu nasarar kashe mafiy yawa daga cikin gungun yan ta’adda da suka harba rokoki ko Bama-bamai a Maiduguri ranar Alhamis daidai lokacinda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke kai ziyara a jihar
Muryoyi ta ruwaito IGP Usman ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da manema labarai jim kadan da suka kammala wata ganawa da shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa ranar Juma’a.
Ya ce yan ta’addan sun harba rokoki a ziyarar shugaban kasar amma cikin taimakon Allah basu samu nasarar cimmma abunda suka so cimmawa ba saboda tsaron da matakan tsaro da aka sanya a jihar ta Borno a lokacin ziyarar shugaban kasar
- Advertisement -
Ya kuma ce shugaban kasa ya basu oda kada su dagawa kowane dan ta’adda kafa