Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuAn tsaurara tsaro a Kano bayan yan daba sun kona ofishin Sanata...

An tsaurara tsaro a Kano bayan yan daba sun kona ofishin Sanata Barau

Daga Muryoyi

An tsaurara matakan tsaro bayan da wasu da ake zargin yan daba ne suka kaiwa ofishin yakin neman zaben Sanata Barau Jibrin hari, mai neman takarar shugabancin jihar Kano a kakar zabe mai zuwa ta 2023.

Jibrin yana daya daga cikin jiga-jigan mambobin APC na G-7 karkashin jagorancin Sanata Ibrahim Shekarau. Kungirar G-7 ta samu gagarumar nasarar a ranar Talata lokacinda wata babbar kotun birnin tarayya Abuja ta amince da zababbun shugabannin ta da aka zaba a gun taronsu sannan ta rusa wadanda bangaren gwamna Abdullahi Ganduje ya zaba.

Wakilin Muryoyi ya ruwaito yan daban sun je a daruruwansu ne lokacinda suka kai farmaki ofishin yakin neman zaben dake akan hanyar Maiduguri a yammacin ranar Laraba. Ginin da abin yashafa, mallakin tsohon ministan kwadago ne Alhaji Musa Gwadabe.

- Advertisement -

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: