Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuAn tsinci gawar Barawo a kasan mota yaje kwance-kwance ta danne shi...

An tsinci gawar Barawo a kasan mota yaje kwance-kwance ta danne shi ya mutu

Daga Muryoyi

Wani abun tashin hankali ya auku a garin Ago Egun dake kauyen Idiroko a cikin karamar hukumar Ipokia ta jihar Ogun bayan da aka wayi gari da ganin wani abun al’ajabi a wani garejin gyaran motoci.

Muryoyi ta ruwaito a ranar Alhamis an ga gawar wani mutum a kasan wata mota dake ajiye ana zargin barawo ne ya je kwance wasu kayan motar sai ta fado ta danne shi sakamakon tangardar da abun daga motar wato JAK ya samu.

Kwamandan yan sa kai na jahar Ogun, Soji Ganzalo, ya ce sun samu rahoto faruwar lamarin inda suka sanar da rundunar yan sanda.

- Advertisement -

A cewarsa an samu spanu da sauran karikiten gyaran motoci bayan an zaro gawar mutumin kuma ana kan gudanar da bicike

Yace motar dadda ce da aka ajiye ta a garejin kuma ana zargin barawon ya je kwance kayan motar ne sai ta danne shi ya kasa fita har ya mutu sakamakon Jak din da yayi amfani dashi ya samu matsala ko ya gurde

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: