Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuAna cigiyar iyayen wannan yarinya mai suna Zainab wacce tace sun zo...

Ana cigiyar iyayen wannan yarinya mai suna Zainab wacce tace sun zo Kaduna biki daga Kano

Daga Muryoyi

Ana cigiyar iyayen wata yarinya yar kimanin shekara 9 da haihuwa wacce ta ce sun zo Kaduna biki daga Kano amma ita tayi batan hanya. A hirar ta da Muryoyi ta ce sunan ta Zainab sunan mahaifin ta Hamisu sannan sunan mahaifiyar ta Amina.

Zainab ta ce sun zo Kaduna biki daga Kano yau kusan kwana Uku aka tsince ta a Unguwan Badarawa, duk wanda Allah yasa ya santa ko iyayen ta ya sanar da su suje gidan Sarkin Badarawa ko gidan Mai Unguwa Malam Ibrahim bayan Asibitin Yara Badarawa Kaduna domin karbar diyarsu.

A yada wannan cigiya har Allah yasa a dace.

- Advertisement -

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: