Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuAna nuku-nukun binciken Biliyan N10 da ta bace a kasafin majalisa -inji...

Ana nuku-nukun binciken Biliyan N10 da ta bace a kasafin majalisa -inji SERAP

Daga Muryoyi

Kungiyar SERAP mai fafutukar yaki da cin hanci da barnata dukiyar yan Nigeria ta nemi Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan da na wakilai Mr Femi Gbajabiamila su gaggauta bincikowa tare da mikawa hukumar yaki da cin hanci domin hukuntawa mutanen da aka samu da laifi wajen bata ko karkatar da ko yin sama da fadi da wasu makudan kudade da suka kai akalla Naira Biliyan 10bn a kasafin majalisun na 2019.

Ofishin akanta Janar na Nigeria ne ya gano babu kudin a cikin rahoton da ya fitar inji SERAP, kuma ta zargi ana nuku-nuku wajen yin bincike akai.

A cikin wata zungureriyar takarda da ta turawa majalisar kungiyar ta zargi majalisun da yin wasu take-taken kaucewa binciken yadda akayi da makudan kudaden watakila domin rufawa wasu asiri.

- Advertisement -

Muryoyi ta ruwaito Kungiyar tayi barazanar daukar matakin shara’a kan majalisun, muddin ta ki daukar matakin bincikowa ko yi mata bayanin batan kudin nan da kwanaki 14.

SERAP a cikin zungureriyar takardar ta yi bayani daki-daki yadda jimullar kudi har Naira N10,051,283,568.82 suka bace a rahoton tattara bayanan binciken kudi na majalisar 2019 wanda ofishin akanta janaral na kasa ya bankado bayan ya bi diddigin yadda aka kashe kudin majalisar a kasafin majalisun Biyu na 2019.

A cewar SERAP haka ma a kasafin 2015, 2017 da 2018 sai da ofishin akanta janar ya bankado yadda fiye da Naira Biliyan N8bn na kudaden yan kasa ya bace ko aka karkatar a kasafin majalisun biyu.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: