Daga Muryoyi
A yayin da miliyoyin yan Nigeria ke tur da Allah wadai kan yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsallake kafarsa ya tafi Lagos bikin kaddamar da littafi ana tsaka da juyayin kashe Gomman matafiya da yan bindiga suka kona kurmus a mota,
Kwatsam kuma sai aka hangi shi kanshi Gwamnan jahar Sokoto wanda abun ya faru a jaharsa, Aminu Waziri Tambuwal shima ya tsallaka ya tafi Lagos bikin karrama Gwamnan jahar Lagos Babajide Sanwo-Olu da akayi a jiya Asabar
Muryoyi ta ruwaito Gwamna Tambuwal tare da ministan Kimiyya da Fasaha na Nigeria Dr. Ogbonaya Onu, suka mikawa Gwamnan lambar karramawa baki har kunne suna raha cikin annashawa da nishadi
- Advertisement -
Taron karramawar wanda akayiwa lakani da Hallmarks (Labour Award 25th anniversary and 2020/2021) ya gudana ne a dakin taro na Oriental Hotel, Victoria Island, Lagos ranar Asabar.
A yanzu haka dai Tambuwal yana cikin jerin na gaba-gaba wajen neman Shugabanci kasa a 2023.