Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuBa mai tausayin Buhari domin shi ya nemi sai yayi Shugabanci --Bisi...

Ba mai tausayin Buhari domin shi ya nemi sai yayi Shugabanci –Bisi Akande

Daga Muryoyi

Tsohon Shugaban jam’iyyar APC na kasa Cif Bisi Akande ya bayyanawa Buhari cewa ba za su ji tausayin sa ba akan zaginsa da ake yi kan tabarbarewar tsaro da koma baya da Nigeria ke fuskanta a halin yanzu domin shi (Buhari ya nemi sai yayi Shugabanci a kasar)

Ya ce zaman lafiya a yanzu yan Najeriya ke so.

Akande ya bayyana haka ne yau Alhamis a wajen bikin kaddamar da littafi kan rayuwarsa da aka sanya wa suna , “My Participations,” wanda ya gudana a Eko Hotel and Suites, Victoria Island a Lagos

- Advertisement -

Muryoyi ta ruwaito tsohon shugaban ya cigaba da zayyana wa Shugaban kasar cewa “kowa na zagin Buhari kuma ana daura masa laifi ne saboda shine Shugaba, dalilin da yasa bana tausayin ka bisa caccakar ka da yan Nigeria ke yi kan rashin tsaro da tabarbarewar kasar kenan.

Bisi Akande a gaban Shugaba Buhari ya cigaba da bayyana wa Shugaban kasar wanda ke zaune a wajen taron cewa “Kai ka nemi zama shugaban kasa saboda haka ka magance matsalar.”

“Mun san kana son kasar, amma muna son zaman lafiya a kasar nan, kuma muna son cigaba. Muna zaginka kan komai da ke faruwa da kasarnan.”

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: