Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuBabu namiji mai lafiyayyen hankalin da zai yiwa mace gorin Aure --ga...

Babu namiji mai lafiyayyen hankalin da zai yiwa mace gorin Aure –ga dalili

Daga Muryoyi

Ra’ayin Abba Adam Isah

Babu Namiji mai lafiyayyen Hankalin da zai yiwa mace Gorin Aure, kodai bashida ƙanwa wacce ta isa Aure Allah bai kawo mata miji ba, to dole za’a same su birjik a cikin danginsa,

Akwai ƙuna sosai a goranta maka abunda ba kaine ka ƙagawa kanka ba,

- Advertisement -

Shi zaman gida ga wasu matan alkairi ne, bature yace “is better to wait long than to marry Wrong” mun kwana da sanin yanzu yadda zamani ya lalace akwai samari da yawa da suke zuwa gurin ƴan mata badan su Auresu ba, kawai anga yarinya ta kawo kai za’a lallaɓa ayi mata wayo,

Kai kuma kana gefe baka san yadda take famar yaƙi da irin wanann samarin ba, kana gani kamar suna zuwa neman Auren ta ne itace bata amincewa, Haka a cikin gida iyayenta zasu hura mata wuta akan lallai ta fito da mijin Aure a cikin samarin da suke zuwa, idan ba Haka ba su zasu zaɓa mata da kansu, idan yarinyar basuda kyakkyawar Fahimta da iyayenta, nan ma wata matsalar ce, kasancewar bazata iya buɗe baki ta gaya musu kalar samarin da suke zuwa gurin ta badan Aure suke zuwa ba wasu buƙatun ne suke kawo su,

Ƙarshe sai Rayuwar yarinya ta kasance kullum cikin tunanin yadda zata samawa kanta mafita, dan kaucewa Auren dole.

Ƙannen mu ne yayyen mu ne, Addu’ar mu suke buƙata ba Gori ba,

Allah ya basu mazaje nagari masu tausayinsu waɗanda zasu riƙe su Amana.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: