Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuBIDIYO: Sarkin Bauchi ya rera wakar "Yesu zai dawo" tare da Kiristoci...

BIDIYO: Sarkin Bauchi ya rera wakar “Yesu zai dawo” tare da Kiristoci a fadarsa

Daga Muryoyi

Sarkin Bauchi, Dr Rilwanu Suleiman Adamu ya gwangwaje da wakar “Yeau Almasihu zai dawo” a lokacin da tawagar kiristocin matan Zumunta suka kai masa ziyarar kirsimeti a fadarsa dake Bauchi.

Sarkin bayan yayi masu maraba yayi jawabin a zauna lafiya da juna kawai sai aka ji ya dora da wakar “Yesu zai dawo” inda nan take Kiristocin suka hau mamaki tare da fashewa da ihu kana suka bishi aka cigaba da wake na yan mintuna.

Dr. Rilwan wanda shine Shugaban Sarakunan Bauchi kana mai daraja ta daya ya sha alwashin barin kofarsa a bude ga duk kiristoci

- Advertisement -

Tawagar ta kiristoci ta ziyarceshi ne a karkashen shugaban CAN na Bauchi Rev. Abraham Damina Dimeus

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: