Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuBuba Galadima yace sai ya jagoranci babbar zanga-zanga idan aka kara kudin...

Buba Galadima yace sai ya jagoranci babbar zanga-zanga idan aka kara kudin mai

Daga Muryoyi

Tsohon na hannun daman Shugaban kasa Muhammadu Buhari, kana gogaggen dan siyasa Alhaji Buba Galadima yayi kira ga yan Nigeria su mara masa baya suyi zanga-zangar bore muddin aka kara farashin litar mai daga N165 zuwa N340.

Alhaji Buba a tattaunawarsa da majiyar Muryoyi yaji takaicin wannan kuduri na Gwamnatin Buhari inda yayi kira ga jama’a “Kowa ya zo mu taru mu hada kai mu yaki wannan karin kudi. Ya shafe ni ya shafe kowa”

Muryoyi ta ruwaito Buba na fadin cewa a shirye yake ya jagoranci zanga-zangar. Ya kara da cewa abun da ke masa ciwo shine yadda wasu kafafen yada labarai ke jawowa Buhari farin jini ta hanyar kabilantar da abu duk idan ya faru a Nigeria

- Advertisement -

“Sai mun gama da Buhari har mun kai shi kasa zamu yanka sai kaji wasu jaridun sun danganta matsalar da bangaranci wanda haka ke jawowa Buhari farin jini” Buba ya ce idan an tunkari matsala gaba gadi a daina bangarantar da ita ko kabilantar da ita domin yin hakan na kashewa sauran kabilu guiwa su janye jiki su kasa shiga a fafata da su.

Buba na korafi ne ga yan jaridun kudu dake yawan sauya matsala su bangarantar da ita ko kabilantar da ita wanda hakan ke sa yan Arewa na marawa Buhari baya “Kada ku ce Buhari dan Arewa ne ko Buhari Musulmi ne” wannan na jawo rarrabuwar kawuna har ka ga ya samu magoya baya inji Shi

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: