Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuBuhari ba shugaba bane! ..."har da cewa indai da imani a zuciyar...

Buhari ba shugaba bane! …”har da cewa indai da imani a zuciyar mutum ko da kwayar zarra ne, toh bazai ki Buhari ba”

Ra’ayi Najibullahi Danjuma Musa

Allah ya sani Kuma shine shaida, dama wallahi nasan Buhari bazai iya mulkin kasarnan ba, bashi da tausayi, bashi da abinda bature yake Kira “empathy” (jin yanayin da mutane suke ciki kamar Kaine aciki).

Duk Wanda ya sanni yasan tun 2015 banyi Buhari ba, kuma naji bakin ciki sosai da ya kada Goodluck Jonathan. Duk a cikin qualities na shugabanci guda daya Buhari yake dashi, shima yanzu ya samu tangarda shine “Gaskiya”, duk gaskiyarka idan baka iya dabarun mulki ba, za’a Sha wahala.

Iyayenmu sun bamu labarin irin bala’in da aka shiga a mulkinsa na farko, mafi munin labarin da naji shine, canjin kudi da akayi a lokacinsa cikin sati daya, don kawai ya karya masu kudi a lokacin. Abinda yasa talakawa suke son Buhari ko a wancan lokacin Bai wuce yadda yake Kama tattalin arzikin masu arziki ya balla ba. Wani bawan Allah Yana bani labari yace, lokacin da akayi canjin kudi, har aka gama wadanda suke surkukin kauye basusan ma anyi ba, saidai kawai mutum ya tattaro kudadensa ya shigo sayayya sai yaji ance an daina karbar irin kudin da yazo dasu. Ba yadda ba’ayi ba Buhari ya janye wannan tsarin yaki, har sai da takai babu wani zabi face a hambareshi.

- Advertisement -

Lokacin da akazo zaben 2015 Kowa yasan Good luck Jonathan yayi sakaci a harkar tsaro Amma abisa bayanan da na samu game dashi nasan wallahi bazai tsinana komai ba. Nayi kokarin Wayar da Kan mutane wadanda muke tare Amma Kowa idonsa ya rufe. Daga Mai kafirta ni, sai mai tsinuwa da muggan kalamai. Ban taba damuwa ba, domin nasan Rana Bata karya, Kowa zaiji a jikinsa.

Akwai wani abokina da mukayi hostel daya, saboda sanin matsayata game da Buhari, haka kawai zai daga Wayar karya, ya dunga cewa “Ay Babu Mai son Buhari sai mumini, Babu Mai kinshi sai muna fuki” ko kuma yace “Kowaye kaga Yana so Good luck ya koma mulki ka jefa Masa kaulasan” wani lokacin Kuma yace “indai da imani a zuciyar mutum ko da kwayar zarra ne, toh bazai ki Buhari ba”.

Abin mamaki, rannan mun hadu dashi , kawai yazo ya rike hannuna, yace Mal. Najib ashe Kai waliyyine, wallahi Kai waliyyine, duk abinda ka fada Mana a makaranta game da tsohonnan gashi muna gani Yana ta faruwa. Na hade rai nace me tsohon yayi? Duk kokarin da yakeyi ku bakwa gani? Sai yayi sororo yace ban gane ba, nace meye baka gane ba?, Sai yace Wai ka dawo son Buhari ne? Nace kwarai kuwa ay yanzu ma Istighfari nakeyi na kinsa da kuma kalaman da nayi Kansa lokacin zaben 2015. Na Kara da ce Masa Buhari Yana iya kokarinsa sune dai basa gani, sannan nace indai Yana son Cigaban kasa dolensa yayiwa baba Buhari Addu’a. Kuma na hade rai, ya kalleni ya kura min Ido yaga ba Wasa a fuskata. Kawai sai ya sakeni yace toh Allah ya kyauta nace Ameen.

Gaskiya talakawa munyi kuskure mun riki Buhari a matsayin shine zai cecemu, ya bamu walwala da saukin rayuwa, muka mance Mai Kowa Mai Komai S.W.A.

Allah ka yafe Mana, ya Allah ka kawo Mana sauki.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: