Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuBuhari ya umurci jami'an tsaro su gama da duk yan ta'adda kafin...

Buhari ya umurci jami’an tsaro su gama da duk yan ta’adda kafin 2023

Daga Muryoyi

Shigaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa hafsoshin tsaron Najeriya sabon umurni su ragargaji duk yan ta’adda da suka addabi kasar kafin barinsa ofis a 2023.

Musamman mayakan ISWAP, Boko Haram da sauransu da suka addabi jihohin Arewa maso Gabas.

Muryoyi ta ruwaito shugaban ya bayar da wannan umurni ne a yayin ganawarsa da shuwagabannin tsaro a fadarsa dake Abuja.

- Advertisement -

Hakanan a jawabinsa na bikin Kirsimeti shugaban kasar ya baiwa yan Najeriya tabbacin cewa da yardar Ubangiji duk matsalolin da kasar ke fama dasu zai wuce zai zama tarihi kamar yadda kasar ta samu kanta a wasu mawuyacin hali a baya amma daga baya komi sake daidaita

Shugaban yaji takaicin yadda har mayakan ke iya kaia hare-hare a yanzu don haka ya baiwa hafsoshin tsaron umurni kada a sake bari wani dan ta’adda ya karbi ko taku daya na kasa a cikin Najeriya

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: