Buhari yace Korona ta yiwa Gwamnatinsa cikas ya kasa magance matsalar tsaro, tattalin arziki da yakar rashawa

Daga Muryoyi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce cutar Korona ta yi wa Gwamnatinsa babbar illla har ya kai ga abun ya shafi yakin da yake yi da masu cin hanci da rashawa da kuma haddasa tabarbarewar tsaro a Nigeria,

Buhari ya fadi haka ne a jawabin da yayi a bikin ranar Nigeria a wajen taron kasuwancin da fasaha da ake yi yanzu haka a hadaddiyar Daular Larabawa mai taken “EXPO DUBAI 2020” a ranar Juma’a kamar yadda sanarwar da kakakin shugaban kasar Femi Adesina ya sanar.

Muryoyi ta ruwaito, Mista Buhari na cewa wajibi ne shuwagabannin duniya su hadu domin yi wa korona rubdugu,

- Advertisement -

Domin a cewarsa cutar ta yiwa kasashen duniya illa, kamar yadda tayi wa Nigeria, kodayake Shugaban kasar ya ce duk da haka Gwamnatinsa tayi namijin kokari wajen daidaita al’amurra amma dai cutar ta kassara Gwamnatinsa a fannin yaki da cin hanci da rashawa da fannin tsaro da kuma tabarbarewar tattalin arziki.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: