Daga Muryoyi
Shugaba Muhammadu Buhari ya mika sakon jajensa ga gwamnatin Amurka da mutanen kasar bisa iftil’in guguwa da ta kashe sama da mutum 100 a jihohi Amurka shida
Muryoyi ta ruwaito Buhari na cewa ya damu kwarai kan yadda gidaje da makarantu da wuraren sana’o’i da asibitoci da dukiyoyin Amurkawa suka lalace a sakamakon guguwar.
Shugaban a don haka ya yi kira ga yan Nigeria su taya sauran mutanen duniya addu’a ga wadanda suka rasa ransu da kuma samun saukin wadanda suka jikkata a sakamkon mahaukaciyar guguwar.
- Advertisement -