Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuDA DUMI-DUMI: Buhari ya tura babbar tawaga Katsina da Sokoto bayan 'yan...

DA DUMI-DUMI: Buhari ya tura babbar tawaga Katsina da Sokoto bayan ‘yan Arewa sun fara zanga-zanga

Daga Muryoyi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Juma’a ya tura wata babbar tawaga zuwa jihohin Sokoto da Katsina domin su kawo masa rahoto cikin gaggawa na abubuwan da ke faruwa da kuma abunda ya kamata ayi.

Muryoyi ta ruwaito Buhari ya tura tawagar ne bayan da jihohin Arewacin suka soma zanga-zanga domin nuna bacin ransu game karin hare-hare dake faruwa a yankunan Arewa.

Muryoyi ta ruwaito tawagar da shugaban kasar ya tura sun hada da babban mai bashi shawara kan harkokin tsaro, Major General Babagana Munguno (Mai murabus) da Babban Sufeto Janar na yan sandan Nigeria, Usman Alkali Baba, da Shugaban DSS, Yusuf Magaji Bichi, da shugaban hukumar tattara bayanai ta kasa Ambassador Ahmed Rufa’i Abubakar da kuma shugaban tsaro na Sojojin Nigeria, Major General Samuel Adebayo.

- Advertisement -

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: