Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuDA DUMI-DUMI: Buhari yayi fatali da sabuwar dokar zaben yar tinke da...

DA DUMI-DUMI: Buhari yayi fatali da sabuwar dokar zaben yar tinke da majalisar ta tura masa yasa hannu

Daga Muryoyi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki amincewa da zaben yar tinke da majalisar dokoki ta tarayya suka aika masa a cikin kundin gyaran dokokin zabe

Majiyoyi masu tushe sun shaidawa Muryoyi cewa shugaban kasar ya nemi yan majalisar suyi gyara kan sabbin dokokin zaben wanda kuma cikin abunda ake so su cire har da batun yar tinke

Bayanai sun nuna Shugaban kasar ya samu bayanin cewa zaben yar tinke zai ci makudan kudade da ake hasashen sun kai Naira Biliyan 500 wanda hakan zai jawo wa kananan jam’iyyu cikas ba zasu iya ba, hakanan kuma zaben na dauke da barazana musamman ta fuskar tsaro.

- Advertisement -

Dama dai an ja daga tsakanin Yan majalisa da Gwamnoni kan zaben na yar tinke wanda Gwamnoni ke adawa dashi su kuma yan majalisa ke so, yanzu dai an zura ido domin ganin yadda zata kaya a zauren majalisa

Majalisar dokokin suna da daman zartar da dokokin idan shugaban kasa yaki amincewa “suna iya jefa kuri’ar amincewa idan an samu 2/3 na sanatoci da kuma 2/3 na majalisar wakilai to shikenan kudurin ya zama doka”

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: