Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuDaga 1 ga Janairu 2022 Facebook zai fara karbar kudin haraji gun...

Daga 1 ga Janairu 2022 Facebook zai fara karbar kudin haraji gun yan Nigeria masu talla a shafin

Daga Muryoyi

Daga 1 ga watan Janairu 2022 yan Nigeria masu amfani da Facebook da Instagram wajen yin kasuwanci za su fara biyan kudadan haraji na 7.5% ga duk tallar da zasuyi a Facebook ko Instagram

Bayanin hakan yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da Meta mai kamfanin dandalin sadarwar Facebook da Instagram ya fitar a ranar Alhamis wanda har Muryoyi ma ta samu kwafin sanarwar.

Facebook ya ce cajin harajin zai shafi kowace irin talla da mutum zai yi a Facebook ko na kashin kai ko na kamfani ko na kungiya.

- Advertisement -

Muryoyi ta rawaito sanarwar ta biyo bayan wani mataki ne da gwamnatin Nigeria ta dauka na tabbatar da kamfanonin sada zumunta na biyan haraji

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: