Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuDalilan dake saka Angwaye kuka a lokacin Aurensu

Dalilan dake saka Angwaye kuka a lokacin Aurensu

Daga Umar Ridwan

A kasar Hausa, Mata aka fi sani da kuka a lokacin aurensu. Kukan da aka fi dangantawa da radadin rabuwa da zama a inuwa daya da iyaye da ‘yan-uwansu, don fara wata sabuwar rayuwa a gidan miji. Har ma a kan danganta duk macen da ba ta yi irin wannan kukan da bikinta ba, da mara kunya, don kuwa ana daukan hakan a matsayin ta kosa a kai ta gidan mijinta ke nan.

A wannan zamanin, sannu a hankali, Maza na kokarin shan gaban mata da irin wannan kukan a lokacin aurensu. Ga mutane da yawa, wannan wani abu ne na banbarakwai, don kuwa a baya, ba kasafai ake ganin maza na kuka a lokacin aurensu a bainar jama’a ba.

_To tambayar a nan ita ce:_

- Advertisement -

Me ke sa Angwayen wannan zamanin kuka a lokacin aurensu?

Akwai mabanbanta ra’ayoyi gameda dalilan da ke sa Angwaye kuka a lokacin aurensu. Jama’a da yawa sun yi ittifaki a kan cewa wannan kuka da Angwayen ke yi na farin ciki ne, wasu kuma na danganta hakan da duk da irin kalubalen da suka fuskanta wajen neman auren, daga karshe dai hakarsu ta cimma ruwa.

Jaridar Muryoyi ta ji ra’ayiyin al’uma danganeda dalilan da ke sa Angwayen wannan zamani kuka a lokacin aurensu:

Zainab Adam Garba cewa ta yi: “Angwaye na shar6an irin wannan kuka ne saboda murnar tsallake siradin sharrin Besty, Cousin da Latecomer”.

A nata ra’ayin, Halima Sa’ad (Biochemist) cewa ta yi ba komai ke sa Angwayen kuka ba illa “irin tsala-tsalan kyawawan kawayen Amarya, wadanda suka fi Amaryar tasu kyau da suke gani, tare da ganin kamar ba su darje ba a zaben da suka yi”.

Shi kuwa Hashim Lawal (Hashlaw) na da ra’ayin cewa “tunanin hidimar Amarya da ya dawo kansu bayan an daura aure ne ke sa Angwayen kuka, yana mai cewa a wannan zamanin cefane da kudin gas din girki kadai ba karamin abu ba ne”.

“Iskanci ne kawai ke sa su kuka” in ji Usman Lawal, inda ya kara da cewa “ai mata aka sani da kuka a lokacin aurensu ba maza ba”.

A ra’ayin Zaituna Abdulrashid “Ragon namiji ne ke kuka a lokacin aurensa, tana mai cewa ko ita da take mace, ta sha alwashin ba abun da zai sa ta yi kuka a lokacin aurenta matukar ba auren dole aka yi mata ba”.

Ita kuwa Sakina Bara’u cewa ta yi “kuka ne na murnar samun Mata ta gari da kyar duba da irin yadda wasu Angwayen ke shan gwagwarmaya da kalubale a lokacin da suke neman auren”.

Da wadannan muryoyi na ma’abota Jaridar Muryoyi da muka tattaro maku, shin a ganinku Angwayen da ke kuka a lokacin aurensu a wannan zamanin suna da kwararan hujjojin yin kukan? Ku bayyana mana ra’ayoyinku ku ma!

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: