Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuDan A Mutun Buhari ya koma Kwankwasiyya bayan an sace danginsa a...

Dan A Mutun Buhari ya koma Kwankwasiyya bayan an sace danginsa a Sokoto

Daga Muryoyi

Da alama wankin Buhariyya ya biyo kan wani dan A Mutum Buhari Surajo Saidu Sokoto da yayi kaurin suna wajen kare shugaban kasar sannan yake adawa da duk mai sukar Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari bayan da yan bindiga suka kai hari kauyensu suka kwashe danginsa fiye da Biyar kuma aka kasa ceto su har sai da suka biya kudin fansa.

Muryoyi ta ruwaito Surajo ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa Jama’a su shaida daga yau (jiya Laraba) ya fice daga tafiyar Buhariyya ya koma Kwankwasiyya

Surajo ya rubuta:
“Yau- Wed 29-12- 2021
“Ni Sirajo Sa’idu Sokoto Sokoto.
“Na Bar Tafiyar Buhariyya.
“Na Koma Tafiyar Kwankwasiyya.
“Sanadiyar Barayi Sun Yi Garkuwa Da ‘Yana Uwana 5.
“Nayi Ta Postin Ina Sanarwa!
“Amma Har Muka Biya Kudin Fansa
“Ba’a Taimakan Ba!

- Advertisement -

Sa’idu a baya yayi ta fadin cewa mulkin Buhari kwalliya ta biya kudin sabulu har ya rika barazana zai jagoranci DSS gidajen masu zanga-zanga ko adawa ko malaman da duk sukayi alkunuti ga Buhari kan tsaro a Arewa

Muryoyi ta ruwaito gabanin sanar da ficewarsa Sa’idu ya rubuta cewa
“A Tarihi Ni Ne Masoyan Buhari.
“Wanda ‘Yan Adawar Siyasar Buhari. “Suka Fi Zagin Iyayensa
Social Media Nigeria!”

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: