Dan wasan Hausa Sani Garba SK ya rasu yanzu

Daga Muryoyi

Muryoyi ta samu labarin rasuwar fitaccen ɗan wasan fina-finan Hausa Sani Garba SK a yau Laraba a Asibitin Muhammadu Abdullahi Wase dake Nasarawa jahar Kano, bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Sani SK ya kai kusan shekara uku yana jinya a tsattsaye, amma rashin lafiyar ta taso masa sosai ne a baya-bayan inda ya shafe akalla mako biyar yana jinya a asibiti.

A baya dai an sha yaɗa jita-jitar rasuwar Sani SK, inda ya dinga musantawa har ma a bidiyo da kansa ma a wasu lokutan

- Advertisement -

Ana sa rai za ayi jana’izarsa a gobe Alhamis

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: