Daga Muryoyi
Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur (OPEC) ta bayyana cewa darajar Nigeria ta sake tashi sama a kasuwar mai ta watan Nuwamba, inda ta zama kasa ta daya a Afrika sannan ta Uku a Duniya.
Nigeria ta samu nasarar ne bayan da ta samu karuwar albarkatun kasa a watan Nuwamba ta rika hako danyen mai akalla miliyan 1.27 a kullum a cikin watan.
OPEC ta bayyana haka ne a cikin rahoton ta na watan Disamba 2021.
- Advertisement -
Muryoyi ta ruwaito sabon rahoton ya nuna Nigeria ta samu karuwar hako gangan mai 47,000 a kowace rana a watan Nuwamba idan aka danganta shi da watan Octoba 2021.
Rahoton ya nuna kasashen Saudiyya, da Iraq, da Nigeria ne darajar su ta kara sama a yayin da kasashen Angola, da Libya da Congo darajarsu tayi kasa a kasuwar danyen man na watan Nuwamba