Daga Muryoyi
Hadaddiyar daular Larabawa ta karrama wani dan Nigeria dreban tazi da shaidar yabo ta girmamawa sakamakon ya mayar da Naira miliyan 12 da ya tsinta a motarsa,
Muryoyi ta ruwaito Abraham ya tsinci Darhami 100,000, (kwatankwacin Naira miliyan 12 a kudin Nigeria) da wani fasinja da ya dauka ya mance dashi a motar.
Dreban tazi din mai suna Abraham Airaodion yana aiki ne da rukunin motocin haya na Sharjah Taxi Cooperation kuma sun bashi satifiket na “amintacce” a ranar Litinin 13, ga watan Disamba 2021.
- Advertisement -