Thursday, March 23, 2023
HomeUncategorizedDuba SuDuk lokacin da naji koke ko a radiyo ko a shafukan sadarwa...

Duk lokacin da naji koke ko a radiyo ko a shafukan sadarwa da kaina nake rubutawa na kaiwa shugaban kasa –inji Pantami

Daga Muryoyi

A wani faifan Bidiyo an gano Ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani Sheikh Ali Isah Pantami yana hira da manema labarai yana bayani akan kokarin da yake yi wajen kai koken talakawa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari

Wannan na zuwa ne dai bayan dubun suka da ake yiwa Ministan na cewa yanzu ya shiga Gwamnati yayi shiru amma a mulkin baya yana cikin na gaba-gaba dake magana akan halin da kasar ke ciki musamman lokacin PDP,

To sai dai Muryoyi ta ruwaito Pantami ya ce suna bakin kokarinsu wajen isar da koken talakawa gun shugaban kasar kuma kwalliya taba biyan kudin sabulu “a bisa tarbiyar da addini ya gindaya, ba zai yiwu ka bawa shugaba shawara ko nasiha kuma ka fito gidan Radiyo ko Talabijin kana fada ba, wannan dalilin ya sanya yace ba zai iya fada ba”

- Advertisement -

Amma dai ya ce a duk lokacin da yaji koke ko a radiyo ko a shafukan sadarwa ko tes ne akayi masa a waya da kanshi yake rubutawa ya kaiwa shugaban kasa shi kuma shugaban kasar zai bayyana masa matakin da zai dauka a gaba.

Ministan ya cigaba da cewa a wasu lokutan yakan shirya malamai na addinin Musulunci sannan Boss Mustapha ya hado Fastoci su zauna da shugaban kasar kuma su bashi shawarwari, ya kawo misali da cewa batun sako Daliban makarantar sakandaren Kankara da batun yajin aikin makarantu na cikin kadan daga irin shawarar da Malaman suka bashi a wani zama na tsawon awa 3 da rabi da aka kwashe anayi a Daura tare da Buhari

Pantami ya kara da cewa kowa ya sani shugaba shi kadai ba zai iya komi ba shi kadai komi karfinsa don haka Buhari na bukatar addu’o’i da goyon bayan yan Nigeria domin kawar da matsaloli da ciyar da Nigeria gaba

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: