Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuDuk namijin da ya kara sakar mace a Kaduna sai ya biya...

Duk namijin da ya kara sakar mace a Kaduna sai ya biya haraji –Mai Rusau

Daga Muryoyi

Shugabar mata ta jam’iyyar APC a jihar Kaduna, Hajiya Maryam Sulaiman Mai Rusau, ta yi kira da babbar murya ga mazajen jihar Kaduna cewa daga yanzu ba zasu yarda a sake cin zarafin ya’ya mata ba a jihar,

Muryoyi ta ruwaito Hajiya Maryam a yayin da take tattaunawa da manema labarai game da cin zarafin ya’ya mata ta ce “Gaskiya akwai abubuwan da zan fada suna da dama, saboda mu yanzu ba zamu kara bari a sake cin zarafin mata ba saboda mata masu daraja ne mu”

Shugabar matar ta cigaba da fadin cewa “Mu masu sanin ya kamata ne, wanda suka san ya kamata, kuma mu masu rauni ne ya kamata mazaje su rika tausaya mana akan abubuwa da dama, saboda ni yanzu ma a jihar Kaduna duk mijin da ya kara sakar mace sai ya biya haraji, don ba zan yarda da sakin mata ba”

- Advertisement -

Sannan ta kara da cewa “Ba zan yarda a ci zarafin mace ba, ba zan yarda ace mace bata da yanci a cikin gidanta ba, duk ba zan dauki wannan ba sai nabi diddigi nabi salsala naji meye dalilin da ya sa har [namiji] ya saki matarshi, ina da wannan kudurin, an daina sakin mata a jahar Kaduna” inji ta

 

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: