Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuEl-Rufai ya kwashe awa 8 yana yiwa dalibai lakca a Kaduna

El-Rufai ya kwashe awa 8 yana yiwa dalibai lakca a Kaduna

Daga Muryoyi

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad el-Rufai, ya kwashe tsawon awa Takwas yana yiwa daliban Kashim Ibrahim Fellows (KIF) lakca kan sha’anin Gwamnati da kuma tattalin arziki a wajen wata bita da KIF din ta shirya ranar Talata a Kaduna.

KIF dai wani shiri ne na musamman da ake yin yan watanni wanda Gwamna Nasir El-rufai ya kirkira kuma ake dibar hazikan dalibai da sukayi fice a fannoni daban-daban na rayuwa daga ko ina a Nigeria domin koya masu dabarun tafiyar da Gwamnati da sauran sha’anin mulki a aikace,

Akan tura yan KIF din ma’aikatu daban-daban na jihar Kaduna suyi aiki kai tsaye da kwamishinoni da shi kanshi Gwamnan domin su gani a aikace sannan su samu gogewa kan yadda ake tafiyar da sha’anin mulki kuma ana biyansu kudade kamar S.As.

- Advertisement -

Muryoyi ta ruwaito a wajen bitar jiya, Gwamnan ya samu rakiyar Darakta Janar na makarantar Kasuwanci ta Kaduna wato “Kaduna Business School”, Dr Dahiru Sani.

Muryoyi ta ruwaito Gwamnan ya baiwa daliban muhimman shawarwari bayan ya kwashe tsawon lokaci rike da alkalami a gaban allo yana tsage masu bayani dalla-dalla kan tattalin arziki, kalubale da kuma matakan tafiyar da Gwamnati.

“Malam ya bamu bayanai da shawarwari masu muhimmanci ta hanyar kawo misalai da kasashe da dama sannan yayi mana bita da nazari akai. Ya kawo mana wasu hanyoyi da za a iya amfani dasu a Nigeria da zasu taimaka sosai wajen bunkasa kasar a cikin kankanin lokaci” a cewar shafin KIF

Daga karshe Gwamna El-Rufai ya baiwa daliban aikin gida wato “Assignment” da zasu je suyi. Kazalika ya kuma basu bayanan irin litattafai da kayan karatu da zasu nema don samun nagartaccen ilimi da nazari kan abubuwan da aka tattauna akai.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: