El-Rufai ya roki yan Kaduna su yarda dashi duk wanda ya dagawa hannu a 2023 su mara masa baya

Daga Muryoyi

Gwamna Malam Nasir El-Rufai ya yi kira ga jama’ar jihar Kaduna kwansu da kwarkwata su yarda dashi su marawa duk dan takarar da ya dagawa hannu a 2023, domin yasan shi ya fi cancanta kuma yasan zai zama Gwarzon Gwamna.

Muryoyi ta ruwaito a wani bidiyo an ga El-Rufai cikin harshen turanci yana cewa “Wasu suna cewa wai abunda mukayi a yanzu ba za yiwu a maida hannun agogo baya ba, to ba haka bane, muddin akayi rashin sa’a wani talasurun dan PDP ya zama Gwamna a jihar Kaduna zai iya maida hannun agogo baya cikin wata Shida. Don haka kada ma kuyi kuskuren zabar PDP a 2023.”

Gwamnan ya cigaba da cewa “Muddin aka zabi PDP to an maida hannun agogo baya, kuma a cikin kankanin lokaci komai zai lalace kamar a shekarun baya.”

- Advertisement -

“Sannan don Allah idan muka tsaida dan takara a APC kuma na aminta da shi to ku yarda dani ku karbe shi hannu bibbiyu ku zabe shi, domin wannan dan takarar nayi amanna jajirtacce ne wanda zai rike amanar jihar Kaduna daga 2023 kuma zai yi aiki tukuru” inji Gwamnan

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: