Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuEl-Rufai ya sake yin sabbin nade-nade bayan ganawarsa da Buhari

El-Rufai ya sake yin sabbin nade-nade bayan ganawarsa da Buhari

Daga Muryoyi

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya nada sabbin shuwagabanni da mambobin gudanarwa na cibiyoyin ilimi da lafiya, da suka hada da Jami’ar jihar Kaduna (KASU), Nuhu Bamalli Polytechnic, College of Education, Gidan Waya, da kuma College of Nursing and Midwifery sannan sai Asibitin Barau Dikko.

Sanarwar da fadar Gwamnatin jihar ta fitar dauke da sanya hannun kakakin Gwamnan Muyiwa Adekeye ya bayyana cewa an nada Hussaini Adamu Dikko a matsayin shugaban gudanarwar KASU, sai Ismail Sanusi Afieza, Dr Tanimu Muazu Meyere, Habiba Sani da Charity Shekari a matsayin mambobinsa.

Muryoyi ta ruwaito an nada kuma Dr. Ishaya Dare Akawu a matsayin shugaban gudanarwar Nuhu Bamali Polytechnic sai Haruna Uwais da Mrs Gladys Goje da Dr Salisu Garba Kubau a matsyin mambobinsa.

- Advertisement -

Sanarwar ta kuma ce an nada Professor Binta Abdulrahman a matsayin shugabar gudanarwar kwalejin ilimi wato College of Education, Gidan Waya, sai Kabiru Ajuji, Masa’udu Doki Igabi, Bayie Joseph Dauda a matsayin mambobinta.

Gwamna Nasir El-rufai ya kuma nada Prof. Andrew Suku a matsyin shugaban kwalejin ilimin Likitanci da Unguwar zoma ta College of Nursing and Midwifery sai Dr Amina Abdulwahab, Prof. IK Zubairu da kuma Rahila Gajere a matsyin mambobi.

Dr Abdulrahman Sambo kuma shine Gwamnan ya nada a matsyin sabon shugaban gudanarwar Asibitin Barau Dikko a yayin da Mohammed Sani Dalhatu, Gambo Mohamed Gadan Gaya, Mrs Margaret Audu, Prof. Idris Suleiman, Prof. Kabiru Musa Yusuf, da Dr Anthony Friday Shemang a matsayin mambobinsa.

Sabbin nade-naden na zuwa ne dai kasa da awa 24 da Gwamnan ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja a ranar Talata

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: