Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuEl-Rufai yasa a karawa ma'aikatan jihar Kaduna albashin wata Daya kyauta

El-Rufai yasa a karawa ma’aikatan jihar Kaduna albashin wata Daya kyauta

Daga Muryoyi

Gwamnatin Kaduna ta ware Naira Biliyan N1.382bn domin rabawa a matsyin kudaden alawus din karshen shekara ga ilahirin ma’aikata Gwamnati dake jihar.

A wata sanarwa da kakakin Gwamnan ya fitar Muyiwa Adekeye yace za a karawa kananan ma’aikata karin albashin wata daya a matsyin alawus a yayin da su kuma manyan ma’aikata za a kara masu kashi 30% na albashinsu a matsayin nasu alawus din.

Muryoyi ta ruwaito El-Rufai yayi wa ma’aikata wannan karamcin ne domin gode masu da kuma kara masu karfin guiwa

- Advertisement -

A karkashin tsarin ma’aikata daga matakin albashi na 1 zuwa na 7 zasu samu kashi 100% na albashinsu a matsayin alawus. Sai kuma yan matakin albashi na 8 zuwa na 13 zasu samu karin kashi 40%, sannan sai manyan ma’aikata yan matakin albashi na 14 zuwa sama zasu samu karin kashi 30%.

Dama dai a watan Satumba 2019 Gwamnatin Kaduna ta zama jiha ta farko da ta fara biyan sabon mafi karancin albashi. Kana ta kara kudaden yan fansho zuwa mafi karancin N30,000 a wata.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: