Daga Muryoyi
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje yace rikicin dake faruwa yanzu a jam’iyyar APC ta jihar Kano rikici ne na cikin gida wanda kuma ba sabon abu bane duk cikin ado ne na dimokuradiyya, don haka ba zai jijjiga shi ba
Gwamnan ya jaddada cewa ba zai bari rikicin ya dauke masa hankali daga cigaba da gudanar da ayyukan cigaban jihar Kano ba
Muryoyi ta ruwaito Ganduje yayi wannan jawabi ne yau Lahadi a wajen taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da ya gudana a fadar Gwamnatin jihar Kano
- Advertisement -
Taron ya samu halartar yan majalisar dokoki ta tarayya daga jihar Kano su 20 da shuwagabannin kananan hukumomi na jihar Kano su 44 da Sanata Gaya da kuma yan majalisar dokoki ta jihar Kano su 28
Muryoyi ta ruwaito an kada kuri’ar amincewa da Gwamnan a matsayin jagora a yayin taron