Daga Abbakar Aleeyu Anache,
Gwamnatin Jihar Bauchi ta ce za ta raba bashin Naira miliyan 500 ga ƴan kasuwa da masu ƙananan sana’o’i domin bunƙasa ƙanana da matsakaitan sana’o’i, SMEs a jihar.
Khalid Ningi, Kataimaki na Musamman ga Gwamna Bala Mohammed kan Harkokin Tallafi ne ya baiyana hakan a tattaunawar da ya yi da Kamfanin Daillancin Labarai, NAN a yau Juma’a a Bauchi.
Sai dai kuma Ningi bai yi ƙarin bayani a kan yawan sana’o’in da za su amfana da bashin ba.
- Advertisement -
Amma kuma ya ce tuni a ka saki kuɗaɗen ta wasu ba kuna domin a hanzarta aiwatar da shirin.
Ya ƙara da cewa gwamnatin ta yi duba ga jinsi, inda za ta samar da daidaito na jinsi a wajen raba bashin domin a samu wakilcin kowanne ɓangaren domin samun cikakkiyar nasarar tsari .
Ya kuma ƙara da cewa gwamnatin jihar da haɗin gwiwa da Gidauniyar Ɗangote sun naira miliyan 200 ga mata masu ƙananan sana’o’i a jihar, inda ya ce kowacce mace da ta amfana da tallafin ta samu Naira dubu 10.