Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuHukumar Hisbah a Kano zata gayyaci iyayen Shatu Garko kan shigarta gasar...

Hukumar Hisbah a Kano zata gayyaci iyayen Shatu Garko kan shigarta gasar Sarauniyar kyau

Daga Muryoyi

Hukumar Hisbah a jihar Kano zasu gayyaci iyayen budurwar nan yar jihar Kano Shatu Garko da ta lashe gasar Sarauniyar kyau ta bana wato Miss Nigeria

Muryoyi ta ruwaito Shugaban Hisbah na jihar Kano, Sheikh Harun Ibn Sina ne ya bayyana hakan inda yace sun bincika asalin budurwar kuma sun gano tabbas yar Kano ce don haka zasu gayyaci iyayen ta domin jin yadda akayi ta shiga wannan gasa wacce ta sabawa shara’a

A cewar Harun zasu yi masu nasiha tare da Jan hankalinsu su gane irin illar da wannan abu zai jawo mata a addinance “domin gasar haramun ce ta sabawa koyarwar addinin musulunci” saboda bayyana tsairaici ce da kuma rashin kunya

- Advertisement -

Muryoyi ta ruwaito Kwamndan ya jawo ayoyi a cikin kur’ani domin kafa hujja kan haramcin sannan ya ja kunnen kada sauran yan mata su fara kwaikwayon ta.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: