Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuIdan Kayan matan ki yana aiki ya akayi auren ki ya mutu...

Idan Kayan matan ki yana aiki ya akayi auren ki ya mutu –Wani Attajiri ya kalubalanci Jaruma

Daga Muryoyi

Biloniyan dan kasuwa a Kudu, Ned Nwoko yayi zazzafan martani kan labarin da shahararriyar mai sayar da kayan mata, Hauwa Saidu wacce aka fi sani da Jaruma tayi na cewa kayan matar da ta bawa amaryarsa ne yayi tasiri akansa har ya saki uwargidansa yar kasar Morocco, Laila Charani.

A martanin da yayi wa Jaruma, Mista Ned ya ce inda kayan matan ta yana tasiri to mai ya hana ta rike mijinta dashi, ta bari har aurenta ya mutu

Muryoyi ta ruwaito Rikici ya kunno kai tsakanin Mista Ned da uwargidansa yar kasar Morocco Laila Charani bayan ya auri jarumar Fina-finai Regina Daniels, har ta kai ga ya saki uwargidansa tasa.

- Advertisement -

Nan da nan Jaruma ta yada cewa hadin kayan matan da ta bawa Regina ne ya ruda shi.

A sanarwar da ya fitar hamshakin dan kasuwar ya musanta hulda da Misis Hauwa (Jaruma), Inda kayan matan ta yana tasiri me yasa ta bari auren ta mutu da mijin ta Isabor shekaru kadan da yi.

Tun a bara ne dai aka fallasa cewa auren Jaruma da Isabor ya mutu har akayi ta cece-kuce

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: