Daga Muryoyi
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta aikewa shugaban kasa Mohammadu Buhari martani na wasikar da ya tura mata na neman shawara kan ya amince ko kada ya amince da dokar gyaran zabe musamman batun yar tinke.
Hukumar zaben ta shawarci shugaban kasar ya sanyaw dokar hannu.
Muryoyi ta ruwaito daga Majiya mai tushe INEC ta gayawa Buhari cewa sanya wa dokar hannu zai kara inganta sha’anin zabe a Nigeria.
- Advertisement -
A ranar 29 ga watan Nuwamba 2021 ne dai Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika da wasika zuwa ga Shugaban hukumar zaben INEC, da mataimakin shugaban kasa, da ministan Shara’a, da ministar kudi da kuma Babban sufeto janar na yan sandan Nigeria ya basu zuwa ranar Juma’a 3 ga watan Disamba su bashi shawara game da dokar gyaran zaben wanda majalisar tarayya ta tura masa tana neman ya sanyawa hannu.
A nata shawarar INEC ta ce kwaskwarimar da akayi wa dokokin zaben zai matukar taimaka mata, misali kamar batun sake nazarin sakamakon zaben da hukumar ta bayyana a karkashin tilastawa da kuma batun aikawa da sakamakon zabe ta intanet da sauransu.
Zai taimaka musamman a yanzu da INEC din ke shirin gudanar da zaben babban birnin tarayya, zaben Gwamnan Ekiti da Osun da kuma uwa uba babban zaben 2023 dake tafe.
Muryoyi ta ruwaito shugaban kasar yana da daga nan har zuwa 19 ga watan Disamba ya amince ko watsi da dokar.
Sai dai masu hasashen na ganin akwai babban aiki idan har bai sanya hannu ba zuwa ranar 15 ga watan Disamba majalisar zata tafi hutun karshen shekara sai kuma mako na uku na watan Janairu 2022 zasu dawo hutun.