Daga Muryoyi
Gwamnatin tarayya ta ce daga ranar 24 ga watan Disamba 2021, zuwa 4 ga watan Janairu 2022 shiga jirgin kasa kyauta ne a duka fadin kasarnan.
Sanarwar hakan ta fito ne a yau Juma’a daga Daraktan hukumar kula da jiragen kasa NRC, Mista Fidet Okhiria,
Muryoyi ta ruwaito sanarwar ta bukaci jama’a dake son shiga jirgin kasa don yin zirga-zirga su garzaya tashoshin jiragen su nemi tikitin shiga jirgin za a basu a kyauta ba tare da kashe ko sisi ba har zuwa wa’adin da aka gindaya.
- Advertisement -