Daga Muryoyi
Bayan da labarin zuwan ta kasar Amurka ya karade kafafen sadarwa, Ministar walwala ta leka Dubai wajen taron fasaha da ake kan yi a Dubai daular UAE
Bashir Ahmad ne ya wallafa hoton a shafinsa na Facebook kuma yace yau aka dauke shi.
Kodayake dama ba tun yau fadar shugaban kasa ke wallafa hoto ba amma daga bisani a iske ba haka bane alal misali aikin wuta na mambila, an ga yadda Bashir Ahmad da su Garba Shehu suka wallafa hoton aikin amma kwatsam bayan shekaru aka gano ba haka bane.
- Advertisement -
Batun zuwa haihuwa kuma har yanzu ministar bata karyata ko gasgata rade-radin ba. Dama ba ba sabon abu bane domin matan manya kan je kasashen waje tun ciki na karami su zauna a cen har sai ya kai munzalin haihuwa.
A cikin makon nan ne Muryoyi ta ruwaito maku yadda wasu jaridun kasar nan da suka hada da New Telegram, Sahara Reporters da sauransu suka tsegumta cewa ministar ta fita kasar Amurka haihuwa