Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuKaduna zata shigar da daliban makarantun sakandiri cikin tsarin inshorar lafiya

Kaduna zata shigar da daliban makarantun sakandiri cikin tsarin inshorar lafiya

Daga Muryoyi

 

Hukumar bayar da gudunmawar lafiya ta jahar Kaduna tace ta kammala shiri na shigar da daliban makarantun sakandire cikin tsarin inshorar lafiya nata.

 

Shugaban tawagar hukumar Abubakar Sa’idu ne ya bayyana hakan a ranar Asabar a Zariya a wajen rufe taron yini biyu na bitar kafafen yada labarai na tsawon kwanaki biyu, wanda kungiyar ceto yaran kasa da kasa ta shirya.

 

Wakilin Muryoyi ya ruwaito Sa’idu yace za’a shigar da daliban ne a karkashin shirin inshorar lafiya na makarantar sakandire na KADCHMA, inda za’a fara da daliban makarantun kwana.

 

- Advertisement -

Yace a karkashin shirin, za a karfafa dakunan shan magani a makarantun sakandire domin samar da kiwon lafiya ga dalibai. Ya kuma kara da cewa a lokacin hutu, daliban da aka zaba zasu ziyarci cibiyoyin kiwan lafiya mafi kusa dake karkashin shirin dan samun damar samu kulawa a koda yaushe.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: