Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuKalli martanin da NUT tayi game da korar malamai 233 da Gwamnatin...

Kalli martanin da NUT tayi game da korar malamai 233 da Gwamnatin Kaduna ke shirin yi

Daga Muryoyi

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce babu gudu ba-ja da baya sai ta yi wa malaman jihar su 12,254 jarabawar gwaji da kuma horo wanda daga watan Janairun 2022

Sanarwar hakan ta fito ne daga shugaban hukumar ilimi ta bai daya Tijjani Abdullahi a lokacinda yake sanar da batun cewa zasu kori wasu malamai 233 da suka gano an dauke su aikin malumta ne da takardun bogi na makaranta,

Muryoyi ta ruwaito shugaban SUBEB din na cewa sun tura takardun shaidar kammala karatu na malami 451, Zuwa ga makarantun da suka ce sunyi. Amma kuma zuwa yanzu an samu martani daga makarantu 9 cikin 13 inda makantun suka ce basu san malaman ba, ba dalibansu bane kuma basuyi karatu a makarantun da suka ce sunyi ba, don haka jabun satifiket suka ne suka bayar.

- Advertisement -

Gwamnatin jihar Kaduna harwayau ta lashi takobin hukunta malaman.

 

MARTANIN Kungiyar malamai…
To sai dai kungiyar malamai ta NUT tace ce ba zata lamunci wannan mataki da SUBEB ke shirin dauka na korar malamai 233 ba.

NUT ta umurci Malaman da abun ya shafa cewa indai sun san takardunsu ba jabu bane su garzaya hedkiwatar NUT ta Kaduna su kai takardun nasu kungiyar zata bincika muddin ta samu cewa takardun malaman na gaskiya ne to dole sai an mayar dasu bakin aiki.a

Muryoyi ta ruwaito NUT na cewa ba zata goyi bayan malaman da aka tabbatar takardunsu na bogi bane amma dai zata tabbatar anyi masu adalci

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: