Daga Muryoyi
Yau shekara guda kenan da Gwamnatin jihar Kano ta bayyanawa duniya cewa Jami’ar East Carolina da ke Amurka ta bai wa Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje matsayin Farfesa sakamakon abin da ta kira “ƙwarewarsa wurin gudanar da mulki na gari da kuma inganta rayuwar al’umma”.
A sanarwar da kakakin Gwamnan, Abba Anwar ya fitar a lokacin, ya ce gwamnan zai fara bayar da shawarwari ga ɗalibai masu digiri na uku, da kuma ƙananan malamai.
Haka kuma gwamnan zai shige gaba wurin bai wa cibiyar biincike ta jami’ar shawarwari kan batutuwan ilimi da kuma gudanar da gwamnati ta intanet da kuma harkokin ƙasa da ƙasa.
- Advertisement -
To sai dai tun a watan Disamba 202 da akayi wannan sanarwa har zuwa yau 2 ga watan Disamba 2021 kusan ana iya cewa ko Amurka ma Gwamna Ganduje bai je ba ballanatana koyarwa