Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuKotu ta sake tabbatar da bangaren su Shekarau ta ci tarar su...

Kotu ta sake tabbatar da bangaren su Shekarau ta ci tarar su Ganduje 1M

Daga Muryoyi

Babban Kotun Abuja wacce APC bangaren Ganduje suka daukaka kara ta yanke hukunci inda ta sake jaddada zaben da bangaren su Shekarau sukayi a matsayin shine halastaccen zabe, sannan kuma ta kori karar

Muryoyi ta ruwaito da yake yanke hukunci a yau Juma’a Alkalin kotun mai shara’a Justice Hamza Muazu ya umurci bangaren Ganduje su biya bangaren Shekarau tarar Naira Miliyan Daya na bata masu lokaci,

Kotun ta kara jaddada cewa zaben APC da bangaren Sanata Ibrahim Shekarau suka gudanar na kananan hukumomi da kuma mazabu da gundumomi ya halasta kuma su ke da damar zaben shuwagabannin jam’iyya a matakin jaha sannan ta kori karar da su Ganduje suka shigar

- Advertisement -

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: