Daga Muryoyi
Wata Babbar Kotu a jihar Kano a karkashin mai shara’a Tanimu Shehu ta tasa keyar wasu mutane Uku da aka kama bisa satar ATM 1,144 zuwa kurkuku na tsawon wata 6 kowanensu
Muryoyi ta ruwaito an yankewa mutanen hukunci ne a zaman da kotun tayi a yau Litinin a Kano
Wadanda aka kama kuma aka same su da laifin sun hada da, Abdullahi Usman, da Musa Abubakar da Abdulwahid Auwalu, EFCC ce dai ta kama su tsakanin 24 ga watan Nuwamba zuwa 1 ga watan Disamba 2021.
- Advertisement -