Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuKungirar kwadago, NLC za ta kalubalanci El-Rufa'i kan rage ranakun aiki zuwa...

Kungirar kwadago, NLC za ta kalubalanci El-Rufa’i kan rage ranakun aiki zuwa kwana Hudu

Daga Muryoyi

Kungirar kwadago ta Najeriya, NLC reshen jahar Kaduna ta bayyana cewa za ta rubutawa Gwamna Nasir El-rufai wasika don neman karin bayani akan manufarsa ta rage kwanakin aikin Gwamnati zuwa kwana hudu.

A ranar Litinin ne dai Gwamnatin jahar Kaduna ta bayyana cewa daga ranar 1 ga watan Disamba ta sauya ranakun aikin mako zuwa kwanaki hudu banda ma’aikatan fannin lafiya da ilimi.

Shugaban NLC reshen Kaduna, Ayuba Magaji Sulieman ya ce kawo yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnati ko ofishin shugaban ma’aikatan jahar dake shaidawa ma’aikatan jahar cewa Juma’a bata cikin ranakun aiki.

- Advertisement -

Wakilin Muryoyi ya ruwaito daga majiya mai tushe Magaji na cewa sun duba dokokin aikin Gwamnati kuma sun ga sabon dokar da Gwamnan yayi bai tuntube su ba ta sabawa doka. A cewarsa dokar aikin Gwamnati ta fi karfin Gwamna, ko majalisar zartarwa ko majalisar dokoki ta jaha, dan haka gwamnan jaha ko majalisar jaha ko gwamnatin jaha bazasu iyayin wata doka ko ka’ida dangane da hakan.

Abin tambaya anan shine a ina Gwamnan ya samu wannan karfi na aiwatar da wannan dokar? A matsayinmu na wakilan ma’aikata ba’a sanar damu ba kafin aka zartar da wannan dokar ba hakan yana mufin akwai wata manufa akan hakan. Amma dai amsar da Gwamnan ya bayar idan mun aika masa da wasikar ita za ta bamu damar sanin matakin da zamu dauka na gaba

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: