Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuMajalisar dokokin jihar Bauchi ta tsige Kwamishinan Ilimi, Aliyu Tilde

Majalisar dokokin jihar Bauchi ta tsige Kwamishinan Ilimi, Aliyu Tilde

Daga Muryoyi

Majalisar jihar Bauchi ta tsige Kwamishinan ilimi na jahar, Dr. Aliyu Tilde, bisa zarginsa da sukyi masa na yi wa kwamitin ilimi na majalisar rashin kunya a ranar Juma’a da ta gabata.

Muryoyi ta ruwaito daga majiyoyi cewa Majalisar ta dauki wannan mataki ne a zaman ta na ranar Litinin bayan ta tattauna kan yadda Kwamishinan yayi ma kwamitin ilimi na majalisar rashin girmamawa a lokacin da suka gayyace shi ranar Juma’a kan batun zuwa ya kare kasafin kudi na ma’aikatarsa.

Kwamitin wanda dan Majalisa Babayo Muhammad, ke wakilta ya gayawa majalisar cewa Malam Aliyu Tilde ya rika yi masu rashin girmamawa iri-iri har ma yana tambayarsu “su waye su” bayan ya gama bata masu lokaci ya shanya su kusan tsawon awa guda kafin ya zo majalisar.

- Advertisement -

Hakan ya tunzura majalisar inda nan take ta kada kuri’ar rashin amincewa da shi a matsayin Kwamishina sannan suka nada Babban Sakataren ma’aikatar ilimi na jihar Bauchi ya cigaba da rikon kwarya a ma’aikatar kafin Gwamna ya nada sabon Kwamishina.

Yan majalisar dai sun ce sun janye tantancewar da sukayi wa Malam Aliyu Tilde a ranar 17 ga watan Augusta 2021 a matsayin Kwamishina.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: