Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuMiji ya saki matarsa da ya gano ta mallaki N3.6m amma dansu...

Miji ya saki matarsa da ya gano ta mallaki N3.6m amma dansu ya mutu a Asibiti saboda kasa biyan dubu 25 ayi masa aiki

Daga Muryoyi

Wani magidanci ya saki matarsa bayan ya gano zunzurutun kudi har Naira Miliyan Uku da Dubu Dari Biyar (N3.6m) a cikin asusun ajiyar ta jim kadan da dansu ya rasu sakamakon an rasa wanda zai biya Naira N25,000 (dubu Ashirin da Biyar) ayi masa aiki a wani Asibiti da ake jinyarsa.

Muryoyi ta ruwaito magidancin ya gano matar na da kudin ne bayan da ya amshi wayar ta zai amsa kira sai kwatsam ga sautin sako (alert) na bankin ta inda yana budewa ya ga har Naira N3.6m a asusun ajiyar Bankin nata wanda nan da nan ya fusata har ta kai ga ya kore ta daga gidansa.

Majiyoyi sun rawaito matar na cewa ba da gangan taki biyan kudi ayi wa dan nasu aiki ba, a cewar rahoton matar ta dade ita take daukar dawainiyar komi na yaron hatta jinyarsa da komi, lokacinda aka bukaci dubu 25 kudin aiki sai ta ja baya da nufin shima mahaifinsa ya tabuka wani abu domin shima yana da kudi a tare dashi kodayake ta ce “bata san jinkirin zai jawo rasuwar dan nasu ba, kuma tayi nadaman hakan” inji ta

- Advertisement -

Matar wacce aka ki bayyana sunan ta da na mijin ta ji mamakin yadda mijin nata ya fusata daga ya ga kudi a asusun bankin ta “kudina ne kuma da gumin goshi na tara su don haka ban ga wani laifi ba don ina da kudi, shima ai yana da kudi bai kamata kudina ya dame shi har ya kashe auren mu ba”

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: