Ministar walwala ta Nigeria Sadiya Umar Farouq ta tafi kasar Amurka haihuwa

Daga Muryoyi

Wasu bayanai da ke jawo zafafan muhara a halin da ake ciki a kafafen yada labarai na sadarwa shine labarin da ake yadawa cewa Ministar kula da ayyukan jin kai ta Nigeria, Sadiya Umar Farouq ta fice zuwa kasar Amurka domin haihuwa.

Kodayake dai Muryoyi ta nemi jin ta bakin makusantar Ministar amma abun yaci tura amma dai wata jarida The Street Journal ta ruwaito labarin. Dama dai iya cewa ba sabon abu bane domin mafi yawan matan manya a Nigeria kan fice kasashen waje musamman Amurka idan suna da ciki domin haihuwa a cen.

Muryoyi ta ruwaito a watan Satumba 2019 ne dai aka daura auren Ministar da angonta tsohon shugaban hafsoshin sama na Nigeria Air Marshal Sadique Abubakar.

- Advertisement -

An daura auren ne a boye a wani masallaci dake Maitama a babban birnin tarayyar Abuja. An dai daura auren ne ba tare da yayatawa ba kuma ba a sanarwa jama’a ba.

Majiyar Muryoyi THE STREET JORNAL ta ruwaito cewa ana sa ran Ministar za ta komo gida Nigeria bayan ta haihu sannan idan hutun da aka bata na haibuwa ya kare.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: