Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuRashin tsaro ke korar daliban Najeriya fita kasar waje karatu --inji VC...

Rashin tsaro ke korar daliban Najeriya fita kasar waje karatu –inji VC UNIJOS

Daga Muryoyi

Sabon shugaban Jami’ar Jos, UNIJOS, Farfesa Ishaya Tanko ya koka kan yadda yace rashin tsaro ke korar daliban Najeriya zuwa karatu kasar waje, farfesan yayi koken ne a ranar Laraba.

Tanko wanda shine mataimakin shugaban Jami’ar wato VC na goma yayi jawabi ne a wajen rantsar dashi da kuma nadashi wadda aka gudanar a zauren majalisar jami’ar a ranar Laraba.

Yace a shekarun baya jami’o’in Najeriya sunyi tasiri kuma sun samu cigaba amma a yanzu komi ya ja baya sosai saboda halin da ake ciki.

- Advertisement -

Wakilin Muryoyi ya ruwaito Farfesan bugu da kari, ya ce tabarbarewar tsaro da ake fama da ita a kasar nan ta haifar da munanan kalubale inda kusan duk an kama malaman jami’o’i wanda dalilin hakan ya haifar da karuwar yawan daliban dake zuwa karatu kasashen ketare domin samun ilimin gaba da sakandire daga shekara 2011.

Daliban Najeriya da suka tafi jami’ar kasar Ghana kawai sun kusa kai yawan daliban da suka halarci jami’o’in Najeriya da kusan dubu dari.

Sabon mataimakin shugaban jami’ar yace an kirkiro jami’ar ne amatsayin babbar hanyar bunkasa da cigaban al’umma.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: