Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuSabuwar shugaban mata likitoci MWAN reshen jihar Kaduna tayi babban Albishir

Sabuwar shugaban mata likitoci MWAN reshen jihar Kaduna tayi babban Albishir

Daga Muryoyi

Kungiyar mata likitoci ta Nigeria, MWAN reshen jihar Kaduna, ta rantsar da Dr. Zainab Muhammad Idris a matsyin sabuwar shugabar kungiyar wacce zata jagorance ta na tsawon shekara Biyu.

Bikin rantsarwar ya gudana ne ranar Asabar a Kaduna a wajen taron shekara-sheakara na MWAN.

Muryoyi ta ruwaito Dr. Zainab ta lashe takobin yin aiki tukuru domin ganin fannin kiwon lafiya ya inganta a jihar Kaduna, ta bayyana nasarar ta a matsayin wata dama da Ubangiji ya bata domin ta hidimtawa al’umma.

- Advertisement -

Gogaggiyar ma’aikaciyar lafiyar wacce ta shafe fiye da shekara 20 a fagen kiwom lafiya sannan a yanzu take koyarwa a fannin lafiya da magunguna a jam’iar jihar Kaduna wato KASU ta nemi hadin kan mambobin kungiyar domin kaiwa gaci.

Dr. Zainab dai a yanzu haka ita ke jagorancin wani shiri na kula da kiwon lafiya mai suna “Accelerating Nutrition Result in Nigeria in Kaduna State” wanda babban bankin duniya ya kirkiro.

Ta ce Gwamnatin jihar Kaduna na bakin kokarin ta wajen bunkasa sha’anin lafiya a Kaduna kuma su ma zasu yi amfani da duk hanyoyin da suke dashi da kwarewarsu wajen ganin sun taya Gwamnati an kai gaci.

Muryoyi ta ruwaito Dr. Zainab Kwaru ta rike mukamai kala-kala a matkin kasa da jiha da kuma kungiyoyin bayar da agaji na duniya irinsu UNDP, DFID da dai sauransu.

An rantsar da Dr. Zainab Kwaru tare da mataimakiyar ta Dr Aisha Mustapha, da Dr Marufah Lasisis a matsyin Sakatariya sai Dr Amina Jelili, a matsayin mataimakiyar Sakariyah.

Sauran sun hada da Dr. Hassana Yakasai Sakatariyar Kudi, Dr Lubabatu Abdulrasheed, Ma’aji sai Dr Amina Umar, Shugaba shiyyar, Zaria, da kuma Dr Salamatu Akor da Dr Maryam Makarfi a matsayin PRO 1 da PRO 2 da dai sauransu

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: