Daga Muryoyi
Sadiya Haruna matashiyar nan da ta shahara a shafukan sada zumunta, inda take wallafa bidiyo da hotuna na harkokin ƙashin kanta da kuma tare da wasu fitattun matasa a wasu lokutan, musamman a Youtube da Instagram ta kammala ɗaurin-talalar da wata kotun shari’a da ke Jihar Kano ta yi mata.
Muryoyi ta ruwaito an yi wa matashiyar daurin-talala ne bayan da a watan Agustan da ya wuce rundunar Hisbah ta kama ta bisa zargin “yaɗa hotunan batsa” a shafukanta na sada zumunta
Inda Alkalin kotun Mai shari’a Ali Jibrin ya yanke mata hukuncin ɗaurin-talala na wata shida, sannan ya yi umarni ta riƙa zuwa makarantar Islamiyya domin koyon “tarbiyya” da kuma “sanin yadda za ta riƙa mu’amala a matsayinta na Musulma”.
- Advertisement -
Da yake yanke hukuncin, Mai Shari’a Jibrin ya umarci jami’an hukumar Hisbah su riƙa raka ta makaranta sannan su kai masa rajista domin ya tabbatar tana zuwa.
Sai dai a yau Talata ne hukumomi suka fitar da sanarwar cewa matashiyar ta kammala zuwa Islamiyyar kuma a tsawon lokacin da ta kwashe ta koyi kur’ani da Hadisi da sauran litattafai na koyar da tarbiyya da zamantakewa a musulunci